News

Yan Bindiga Sun Mamaye Unguwannin Da Hausawa Suke Da Zama A Jihar Imo

Wasu Rahotanni Da Muke Samu Yanzu-Yanzu Na Cewa, Wasu Yan Bindiga Da Ba’asan Ko Suwanene ba Sun Mamaye Unguwannin Hausawa Dake Jahar Imo.

Kamar yadda jaridar dailytrust ta rawaito cewa anta jin karar harbe harbe da daren ranar litinin a unguwannin na hausawan yayinda sojoji da yan sandan da aka tura yankin ke fafatawa da yan bindigar.

Acikin wani bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, anga mutane nata gudu domin kare kansu daga musayar wuyatar.

Yan bindigar sun arce bayan kasa jure luguden wutar da jami’an tsaron sukai musu.

Babban mai bada shawara na musamman ga gwamna Hope Uzodinma kan harkokin yan Arewa dakuma marasa galiyu, Hon Suleiman Ibrahim Suleiman ya tabbatar da faruwar lamarin.

Inda ya ayyana cewa jami’an tsaron sun dakile harin da yan bindigan suka kawo.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button