NewsPolitics

Malaman Addinin Kirista A Nigeria Sunyi Tattakin Nuna Goyan Bayansu Ga Dr. Isa Ali Pantami A Abuja

Wasu Gamayyar Kungiyoyin Kiristoci a nigeria sunyi tattakin nuna goyan bayan shehin Malamin Addinin Musulimci kuma ministan sadarwan nigeria Wato Dr. isa ali pantami.

Hadaddiyar kungiyar malaman addinin kirista na nigeria wato Forum of Christian Bishops and Clergy Council’ tayi tattakin nuna goyan bayanta ga gwamnatin mohammadu buhari bisa matsayar gwamnatin kan zargin da akewa dr. Is ali pantami.

Kazalika kungiyar ta sanar da hakanne a yayin wani tattaki da tai na nuna goyan bayanta ga Dr. Isa ali pantami a Unity Fountain Abuja, inda kungiyar ta cigaba da cewa, wadanda ke zargin wasu yan tsiraru ne da sam basa san sauye sauyen da ministan keyi a kasar.

Bishop Abel King, shine jagoran masu tattakin yakara da cewa, ya zama dole su fito su bayyana matsayar su bisa zargin da akewa ministan sadarwan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button