Kwana Biyar Kacal Ya Rage Mu Rufe Duk Wani Layin Wayar Da Ba’a Hadashi Da NIN ba, Inji Dr Isa Ali Pantami Ministan Sadarwa Da Bunkasa Tattalin Arzikin Kasa.

Wa’adin da hukumar NCC Ta Nigeria Ta Dauka Karkashin Jagorancin Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Pantami Na Hada Layukan waya da lambar shaidar zama dan Kasa NIN Saura kwana biyar ya kare.

Hukumar Ta NCC ta tunatar da Al’ummar kasar ne a shafinta na twitter Cewa ranar shida ga watan mayu ne ranar da wa’adin da ta diba zai cika.

Inda ta kara da cewa duk wani layin wayar da ba’ayiwa rijista da NIN ba zai daina aiki nan take a nigeria.

Click Here To Drop Your Comment