NewsPolitics

An kama mutanen da ke bai wa Boko Haram bayanai a Neja

An kama mutum tara dake baiwa boko haram bayanai a jahar naija dake arewa maso tsakiyar nigeria Kamar Yadda Gwamnatin jahar tace.

Mai baiwa gwamnan niger shawara akan yada labarai Abdullberqy Ebbo, Yace daya daga cikin mutane taran da aka kama likita ne.

Inda ya cigaba da cewa mutanen sunyi ikirarin bada bayanai ga boko haram game da sojoji.

Ko A Baya Bayan Nan Gwamnatin jahar ta sanar da cewa Qungiyar Boko Haram Ta Kafa Tuta a wasu kananan hukumomi Guda Biyu Dake jahar ta niger.

Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello wanda ya tabbatar da kasancewar Boko Haram a jihar ya ce mayaƙan sun kafa tuta ne a ƙananan hukumomin Kaure da Shiroro.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button