News

Anyi Garkuwá Da Shi A Jirgin Ƙasan Abuja Zuwa Kaduna A Lokacin Da Yake Kan Hanyarsa Ta Tafiya Yiwa Ƙasa Hidima (NYSC)

Anyi Garkuwá Da Shi A Jirgin Ƙasan Abuja Zuwa Kaduna A Lokacin Da Yake Kan Hanyarsa Ta Tafiya Yiwa Ƙasa Hidima (NYSC)

Wannan matashin da kuke gani yana cikin waɗanda aka yi garkuwá da su a jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna, an kama shi ne yayin da yayi sallama da iyayensa da ƴan uwansa da niyyar tafiya ‘NYSC Decumentation’.

Yana farin ciki ya tafi zai yiwa ƙasarsa bauta, gashi anyi garkuwamá da shi, ƙasar da shugabannin ƙasar sun kasa yin komai sama da kimanin kwanaki 120.

Idan kai Uba ne, ka fara yin tunani idan ɗanka ne ya yi waɗannan kwanaki a hannun waɗannan masu garkuwá ya zaka kasance?

Idan kuma Uwa ce, kiyi tunanin halin da za ki kasance idan aka yi garkuwá da ɗaya daga cikin ƴaƴanki tsawon waɗannan kwanaki.

Mu da muke wannan kafa muke tallatawa, tare da kare wasu gwamnatoci, mu ajiye siyasa mu dubi wannan abin. Misali ace akwai iyayenmu, ƙanananmu ko yayyenmu na tabbata mafi ƙarancin damuwar da za muyi ita ce kwanciya tare da tashi dasu a rayukanmu cikin kowacce rana.

Allah ya kuɓutar da su, da sauran waɗanda suke cikin hali irin nasu, mu kuma Allah ya kare mu. Allah ya zaɓa mana shugabanni nagari a kowanne irin mataki, Allah ya saukar mana da zaman lafiya a wannan ƙasa tamu.

©Idon Mikiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button