News

BIDIYO: Ƴan fashin daji sun ɗauke mata da ƴar ta bayan sun gama raba wa marasa ƙarfi zakkar Ramadan a Kaduna

Ƴan fashin daji sun ɗauke mata da ƴar ta bayan sun gama raba wa marasa ƙarfi zakkar Ramadan a Kaduna

Wasu ƴan fashin daji sun sace wata mai taimakon al’umma, mai suna Ramatu Abarshi tare da ɗiyarta Amira, bayan sun raba kyaututtukan watan Ramadan a ƙauyen Mariri da ke Ƙaramar Hukumar Lere a Jihar Kaduna.

Wata majiya mai tushe ta ce ƴan bindigar sun bi bayan Abarshi ne da tsakar ranar Asabar a kusa da Kasuwan Magani da ke Ƙaramar Hukumar Kachia a kudancin jihar Kaduna.

Abarshi, tsohuwar Shugabar Sashen Fasahar Wutar Lantarki ta Makarantar Kimiya da Fasaha ta Kaduna , ta shahara da ayyukan jin kai da samar da zaman lafiya a Kudancin Kaduna.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ya ce bai san da faruwar lamarin ba.

“Kun san ba koyaushe mutane ke kai rahoton irin wannan lamarin ga ‘yan sanda da zarar ya faru ba,” in ji shi.

Ga Karin Bayani Game Da Batun

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button