News

BIDIYO: Ƴan Sanda sun cafke ɗan shekara 18 da ya kashe ƙanwar babarsa a Kano

Ƴan Sanda sun cafke ɗan shekara 18 da ya kashe ƙanwar babarsa a Kano

Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano ta cafke wani mai shekara 18 da haihuwa, Abdulsamad Suleiman, bisa zargin kashe ƙanwar mahaifiyarsa, Rukayya Jamilu ya kuma raunata ƴaƴanta ƙanana guda biyu a gidanta na aure.

Lamarin ya faru ne tun a watan Fabrairu, lokacin da ƴan sanda su ka iske gawar marigayiyar shame-shame cikin jini, bayan mijinta ya kai rahoto cewa ya dawo gida ya tarar da mai-ɗakin nasa a wannan hali da misalin ƙarfe 8 na dare.

Nan da nan Kwamishinan Ƴan Sanda, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya sa a ka garzaya da matar da ƴaƴan nata asibitin Murtala, inda likitoci su ka tabbatar ta rasu, ƴaƴan kuma a ka ci gaba da kula da lafiyarsu.

A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a jiya Laraba da daddare, tuni dai ƴan sanda sun kama wanda a ke zargi, Suleiman, da abokinsa, Mu’azzam Lawan, ɗan shekara 17, dukkan su mazauna unguwar Dorayi Charanci ne.

Kiyawa ya ce an cafke su ne sakamakon binciken sirri da jami’an yan sanda da haɗin gwiwa da na ƴan sandan farin kaya, DSS su ka yi.

Ya ce Suleiman ya amsa laifin sa na bugawa marigayiya Rukayya taɓarya a ka, lokacin da ya kai mata ziyara ya kuma yi yunƙurin sace mata wayoyinta na salula har guda uku yayin da ta ke kwance a kan gadonta.

Ya kuma amsa cewa ya baiwa abokin nasa waya guda ɗaya kyauta, wacce ya sayar da ita N2,000, shi kuma Suleiman ya sayar da sauran biyun kan N12,000.

SP Kiyawa dai ya ce za a gurfanar da su a gaban kotu idan an kammala bincike.

Ya ƙara da cewa Kwamishinan Ƴan Sanda, Dikko ya ci alwashin ci gaba da zaƙulo da hukunta duk wasu masu laifi a jihar Kano, inda sai dai ko su dena, ko kuma su bar jihar.

https://youtu.be/5-26rV5Mn_s


Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button