News

BIDIYO: ɗaliban Da Ya Mutu A Sokoto Bayan Ya Tserewa Yaqin Ukraine da Rasha

Ɗaya daga cikin ɗaliban Najeriya da suka gudu daga Ukraine ya mutu a garinsu na Sokoto da ke arewacin Najeriya.

Babu cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin mutuwar Huzaifa Habibu.

Mahaifinsa Habibu Halilu Modaci ya shaida wa BBC Hausa cewa an kai shi asibiti ne bayan da ya fara kokawa, yana cewa ba ya jin dadin jikinsa kuma bayan da aka ga alamar ya daina cin abinci sosai.

Ɗalibin, mai shekara 22, yana karatun zama likita ne a kasar Ukraine, kuma a shekara mai zuwa ake sa ran zai kammala karatun nasa, sai dai ya dawo gida mako biyu da ya gabata saboda barkewar rikici tsakanin Rasha da Ukraine.

Wannan ne karonsa na farko na dawowa gida ciki shekara uku.

Mallam Modace ya ce ɗan nasa ya shaida ma sa irin mawuyacin halin da ‘yan Najeriya suka shiga a sanadin yakin na Ukraine, da ma yadda suka rika takawa a kafa na lokaci mai tsawo domin ficewa daga kasar.

Har yanzu Najeriya na da ɗalibai kumanin 100 da rikicin ya rutsa da su a birnin Kherson na Ukraine, sai dai ta riga ta kwaso fiye da dalibai 1,500 tun bayan da yakin ya barke a watan jiya.

https://youtu.be/2uQzDVrRRQU

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button