Ɗan Autan Marigayi Sarkin Kano Ado-Bayero, mai shekara 22 ya auri nata 2 rigis

A jiya Asabar ne ɗan marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, mai shekaru 22, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu rigis.

Bayero, wanda ke fama da ciwon huhu, shi ne ɗan autan marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero.

An ɗaura auren yariman da kyawawan amarensa guda biyu, Badi’a Tasiu Adam da Fatima Ibrahim Adam a Masallacin Markaz Imamu Bukhari, Rijiyar Zaki da Masallacin Juma’a na Tsakuwa, Kano.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa an sha ganin yariman lokacin yana yaro tare da marigayi Ado Bayero a kan keken-doki yayin Hawan sallah.

Click Here To Drop Your Comment