News

BIDIYO: Anyi Martani Kan Makarkashiyar Cire Rubutun Ajimi Daga Kudaden Nigeria Da Ake Shirin Yi

BIDIYO: Anyi Martani Kan Makarkashiyar Cire Rubutun Ajimi Daga Kudaden Nigeria Da Ake Shirin Yi

Sanarwar Babban Bankin Nigeria Kan Batun Chanza Fasalin Kudin Nigeria Ta Jayo Cece Kuce.

Idan Baku Manta Ba, A Shekaran Jiya Ne, Babban Bankin Nigeria Ya Sanar Da Chanza Takardun Kudin.

Gwamnan Babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce bankin zai sauya fasalin wasu takardun kuɗin kasar guda uku.

Ya ce babban bankin ya samu amincewar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari domin sauya fasalin takartun kuɗi na N200, da N500, da kuma takardar kuɗi ta N1000.

Ya ƙara da cewa sabbin kuɗin za su fara aiki ranar 15 ga watan Disamba da ke tafe.

Mista mefiele ya ce ”daga yanzu an cire kuɗin da ake karba daga mutane a lokutan da suke zuwa saka kuɗi a banki.

Gwamnan babban bankin ya ƙara da cewa kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen ƙasar ana hada-hada da su ne ba ta hanyar bankin ba.

Ya ci gaba da cewa wannan mataki zai ƙara wa kuɗin kasar daraja.
Acikin Sanarwar da.

Sai Dai Mutane Da Dama Sun Zargin Cewar Ana Kokarin Cire Rubutun Ajamin Jikin Kudin Ne.

Kamar Yadda Zaku Kalla Acikin Wannan Bidiyon.

👇👇👇👇👇👇

https://youtu.be/5pxVK88PCcI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button