News

BIDIYO: Babban Abin Radadi A Gareni Shine, Bani Da Idon Da Zan Kalli Matar Dana Aura

 

BIDIYO: Babban Abin Radadi A Gareni Shine, Bani Da Idon Da Zan Kalli Matar Dana Aura

Babban abin radadi a gare ni shi ne ba ni da ido da zan kalli matar da na aura a baya bayan-nan, sannan ko da ‘yan uwana da mahaifinmu ya haifa a baya na, su ma ban san yadda kamar su take ba duk da cewa muna tare a kullum.”

Saifullah Mukhtar ya gamu da larurar makanta shekara 17 da suka gabata a lokacin da yake dan shekara 16 bayan ya samu matsala a idanunsa yayin da yake zuwa makarantar sakandare a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Cutar makantar dai, ba ta hana Saifullah damar kammala karatunsa na Jami’a ba a Jami’ar Bayero, kuma bayan nan ne ya samu aiki a hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya.

“Da farko, kamar duk wani da iftila’i ya faru da shi, na dauka cewa karshen rayuwata ne ya zo, mun yi duk mai yiwuwa domin samun lafiya amma komai ya ci tura,” in ji shi.

“Sai lokacin da ni da iyayena muka je wurin wani likitan ido a India, sannan yake fada wa mahaifana cewa ba zan sake gani ba, a lokacin ne muka hakura, sannan na yanke shawarar amfani da rayuwata yadda ya kamata ta hanyar daukar karatu da muhimmanci.”

“Na kammala karatun Digiri a Jami’ar Bayero, kuma ban bata lokaci ba na wuce domin yin Digiri na biyu, inda a baya bayan nan na samu aiki a hukumar kula da sararin samaniya ta Najeriya. Wani abin farin ciki ma shi ne na doke har da mutane masu gani da suka nemi aikin a jarrabawar da muka yi.

“Shawarata ga masu lalurar rashin gani irina ita ce, kar su yanke kauna ga rayuwa, na san cewa akwai radadi idan aka ce mutum ba ya gani amma mutane da dama na cikin matsanancin hali da ya fi wannan, je asibiti za ka ga mutane masu lalura ta laka ko kuma mahaukata.”

“Babban abin radadi a gare ni shi ne ba ni da ido da zan kalli matar da na aura a baya bayan-nan, sannan ko da ‘yan uwana da mahaifinmu ya haifa a baya na, su ma ban san yadda kamar su take ba duk da cewa muna tare a kullum.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button