News

BIDIYO: Bello Turji Ya Kaddamar Da Hari Kan Yan Bindiga A Jahar Zamfara Bayan Wani Sulhu Da Sukai Da Gwamnati

Najeriya: Bello Turji ya kaddamar da hari kan ‘yan bindigan Zamfara

Wani kasurgumin dan fashi da makami Bello Turji ya rungumi shirin zaman lafiya na gwamnatin jihar Zamfara a wani yunkuri na kawo karshen ayyukan ‘yan fashi da makami a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana hakan a yayin wani taro kan harkokin tsaro da kungiyar dalibai da wata jami’ar Madina ta shirya a Gusau babban birnin jihar.

Hassan ya yabawa Turji bisa matakin da ya dauka na ajiye ayyukan fashi da makami, da kuma matakin taimakawa wajen samar da zaman lafiya a kananan hukumomi uku da ke kan gaba wajen fuskantar hare-hare ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

A cewar mataimakin gwamnan, tun makwanni biyar da suka gabata ba a samu wata arangama tsakanin Fulani da Hausawa a kananan hukumomin Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi na jihar ba, sakamakon tattaunawar sulhun da aka yi tsakanin bangarorin biyu da ke rikici da juna a jihar.

Gidan talibijin na Channels ya ruwaito mataimakin gwamnan na cewa, kwamitin da Gwamna Bello Matawalle ya jagoranta ya gudanar da taron zaman lafiya da sansanonin ‘yan bindiga tara a gundumar Magami da Masarautar Dansadau na kananan hukumomin Gusau da Maru na jihar domin su daina kai hare-hare ga mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya ci gaba da cewa, Turji wanda Gwamna Bello Matawalle ya yi wa afuwa, a yanzu haka yana kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a yankunan da suka mamaye domin tabbatar da cewa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya dawo jihar.

Karin Bayani: 👇👇👇

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button