Religion

Ana Zargi Sojoji Da Kashe Fitaccen Malamin Addinin Musulimci Sheikh Goni Aisami A Jahar Yobe

Ana Zargi Sojoji Da Kashe Fitaccen Malamin Addinin Musulimci Sheikh Goni Aisami A Jahar Yobe

Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya nuna baƙin-cikinsa da kisan da aka yi wa wani fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Goni Aisami, a ranar Juma’a a Yobe.

Malamin mazaunin Gashua da ke karamar hukumar Bade an zargi sojoji da harbe shi a yankin Jaji-Maji da ke karamar hukumar Karasuwa na jihar Yobe.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Daungus Abdulkarim, ya ce sojojin biyu da suka yi kokarin sace motar malamin bayan harbe shi an damƙesu.

Gwamna Buni a wata sanarwa da ya fitar a Damaturu, ya ce wannan kisa abin takaici ne da alla-wadai, don haka za a binciki lamarin.

Mai Mala ya ce duk wanda aka samu da laifi za su fuskanci hukunci. Sannan ya miƙa ta’azziyarsa zuwa da iyalan marigayin da al’ummar karamar hukumar Bade da ilahirin jihar kan kisan Aisami.

Gwamnan ya bukaci a kwantar da hankali yayinda ake kan gudanar da bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button