News

BIDIYO: Bidiyon Ambaliyar Da Ta Shafi Kauyuka Da Garuruwa 1,500 A Jahar Jigawa Innalillahi wa inna ilaihir raju’un

BIDIYO: Bidiyon Ambaliyar Da Ta Shafi Kauyuka Da Garuruwa 1,500 A Jahar Jigawa Innalillahi wa inna ilaihir raju’un

Kauyuka, Garuruwa 1,500 Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihar Jigawa – Hukumomi

Ambaliyar ruwa da ake samu a wasu sassan Najeriya sanadiyyar matsanancin ruwan sama a kasar na ci gaba da mummunan tasiri ga rayuwa al’umr kasar, musamman mazauna karkara.

JIGAWA, NIGERIA – Yanzu haka dai shugabannin sarautun gargajiya a Jihar Jigawa daya daga cikin Jihohin Najeriyar dake fuskantar ambaliyar ruwa sun fara neman agaji ga talakawan su daga gwamnatoci da hukumomi masu zaman kansu, saboda mawuyacin halin da al’umarsu ke ciki.

Wata kididdiga  da hukumomin Jihar ta Jigawa suka fitar ta nuna gonaki masu fadin hecta kimanin dubu dari biyu ne ambaliyar ruwa ta mamaye a kananan hukumomi 22, yayin da wannan iftila’in ya rusa gine-gine a kauyuka da garuruwa fiye da 1500.

Kananan hukumomin Ringim da Kafin Hausa da Auyo da Birnin Kudu da kuma Dutse na cikin yankunan da wannan ambaliya ta munana ainun.

Wasu daga cikin al’umar Jigawa da ambaliyar ruwa ta yiwa barna sun ce sun yi asarar kayan amfanin gona na miliyoyin naira, tare da rasa gidajen su. Tuni dai shugabanin gargajiya a Jihar suka fara neman a tallafawa wadannan talakawa nasu.

Ya roki gwamnatoci a dukkanin matakai da kuma hukumonin bada agaji su tallafawa al’umar sa, musamman ta fuskar kayan noman rani domin rage radadi ga mutane.

Hakimin gundumar Sindimina duka a yankin karamar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Adamu Mohammed Nakudu ya ce rayuwar talaka a yankin sa na cikin yanayi maras dadi, a don haka ya ja hankalin mahukunta da cibiyoyi masu zaman kan su da su tallafawa Jama’a.

Tuni dai masu kula da lamura ke hasashen cewa, al’umma a Jihohin Najeriya irin su Jigawa ka iya fuskantar kalubalen karancin abinci saboda wannan lamari, amma kwamishinan ayyuka na musamman a Jihar, Alhaji Auwalu Danladi Sankara ya ce gwamnati na daukar matakan samar da kayayyakin noma, musamman irin shuka mai yi da wuri, kamar dankali da kankana domin manoman Jihar su shuka bayan janyewar ruwa a wuraren da yayi ambaliya.

Wani al’amari da ambaliyar ruwa ta zo dashi Jigawa shine yawaitar hadduran kwale-kwale dake salwanta rayukan mutane, lamarin dake girgiza zukatan al’ummar jihar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:

https://youtu.be/IxXpMyR6Qms

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button