News

BIDIYO: Yadda Ake Dauko Gomman Mutanen Da Suka Mutu A Jigawa Sakamakon Ambaliyar Ruwa

BIDIYO: Yadda Ake Dauko Gomman Mutanen Da Suka Mutu A Jigawa Sakamakon Ambaliyar Ruwa

Karin mutane sun mutu a ambaliyar ruwan Jigawa

Rahotanni sun ce an samu karin mutane fiye 29 da suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a Jigawa da ke Najeriya, yayin da ambaliyar ke ci gaba da mamaye yankuna a sassan jihar.

Karin adadin ya sanya yawan wadanda da suka mutu jumilla a ambaliyar ruwan jihar ta Jigawa kaiwa mutane 92, kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Lawal Shiisu ya tabbatar.

Yayin karin bayani, Shiisu ya ce an samu hasarar rayukan gwamman mutanen ne sakamakon dalilan da suka hada da nutsewa cikin ruwa, hatsarin kwale-kwale, da tsawa, da rushewar gine-gine, sakamakon yanayi na saukar mamakon ruwan sama.

Ambaliyar ruwa dai na ci gaba da yin barna a sassan Jigawa inda ta mamaye filayen noma da kuma yankuna da dama na jihar.

A makon da ya gabata hukumar kula da hasashen yanayin saukar ruwan sama ta Najeriya NIHSA ta tabbatar da cewa jihar Jigawa ke kan gaba wajen fama da matsalar ambaliyar ruwa a fadin kasar.

Ta ce kananan hukumomi 16 na jihar ne lamarin ya shafa hukumar ta ce zuwa ranar 7 ga watan Satumba, sama da mutane 72 ne suka mutu tare da hasarar dukiya mai tarin yawa a sassan jihar ta Jigawa.

https://youtu.be/IxXpMyR6Qms

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button