News

BIDIYO: Cike Da Tashin Hankali, Matashi Ya Sanar Da Mutuwar Budurwar Da Zai Aura Nan D Sati 2.

Cike Da Tashin Hankali, Matashi Ya Sanar Da Mutuwar Budurwar Da Zai Aura Nan D Sati 2.

Safiyanu Abubakar ‘dan asalin garin Toro ne a jihar Bauchi kuma ya sanar da mutuwar Rukaiya, wacce zata zama amaryarsa Ya kara da bayyana katin daurin auren wanda za a yi a ranar Juma’a, 12 ga watan Augustan 2022, amma amarya ta ce ga garinku.

Rashin masoyi babban ibtila’i ne da kan fadawa ‘dan Adam, sau da yawa a kan dade ana jinyar zuciya idan ta rasa abinda take so balle a ce mutuwa ce ta gifta. Wani matashi mai suna Safiyanu Abubakar ya wallafa katin bikinsa wanda za a yi a ranar 12 ga watan Augutan 2022 da masoyiyarsa Rukaiya Ibrahim Salihu.

Matashin ya bayyana sanarwar mutuwar budurwarsa wacce zasu angwance tare nan da makonni biyu cike da damuwa a shafinsa na Twitter mai suna @SufyToro.

Kamar yadda katin daurin auren ya nuna, masoyan zasu zama mata da miji a ranar Juma’a wurin karfe 1 na rana bayan idar da sallar Juma’a.

A wallafar matashin yace: “Wacce zan aura ta rasu a daren jiya. Za a daura mana aure a makonni biyu masu zuwa amma a yanzu babu ita. Daga Allah muke, gare shi za mu koma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button