News

BIDIYO: Cikin Kuka Wanda Ya Kashe Hanifa Ya Musanta Rahotannin Da Ake Ta Yadawa Akansa Cewar Yayi Gunduwa-gunduwa Da Gawarta

Wanda Ya Kashe Hanifa Ya Musanta Rahotannin Da Ake Ta Yadawa Akansa Cewar Yayi Gunduwa-gunduwa Da Gawarta

Shugaban Makarantar Noble Kids dake unguwar yan Kaba kwanar Dakata, a birnin Kano, wato Abdulmalik Mohammed Tanko, ya shaidawa Muryar Amurka cewa.

“Ba gaskiya ba ne rahotannin da ake yayatawa cewa, sun yi gunduwa-gunduwa da jikin Hanifa Abubakar bayan ta mutu kafin suka binne ta.

Abdulmalik Tanko Ya Baiyana hakan ne cikin wani guntun bidiyo da akai hira dashi bayan kai shi kotu.

Abdulmalik ya kara da cewa andai lankwasa kafafuwanta ne sakamakon buhun da aka sakata a ciki yayi kankanta.

Kafafuwanta zasu iya lekowa shine dalilin da yasa suka lan-lankwasa kafafun ta yadda bazasu fito waje ba.

Kamar yadda zaku gani cikin bidiyon dake Kasa abdul ya kara da cewa, wannan al’amari da yafaru yasan babu wanda zaiji dadin sa.

Yakara da cewa ai musulmai ne mu yasan iyayenta ma bazasuji dadin abun ba, inda yace daman ya yanke shawarar fallasa kansa da kansa domin a zartar da hukuncin kotu a kansa.

Inda Yakarashe zancensa da cewa tunda kaga nayi wannan haka ai inada bukatar kotu ta aiyanar da Adalci irin nata

Gadai Bidiyon nan ku Kalla

https://youtu.be/cj5BpepI66A

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button