News

Yaushe Sauran Mutanen Da Ake Kashewa A Arewa Za Su Samu Gata Irin Na Hanifa? Anfara Korafi Kan Nuna Alhinin Kisan Hanifa

Yaushe Sauran Mutanen Da Ake Kashewa A Arewa Za Su Samu Gata Irin Na Hanifa?

Daga Muhammad Sani Hamza Yarima Giwa, Kaduna

Tun farko mun yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa wannan yarinya tun daga lokacin da abun ya baiyana muka sani.

Sannan kuma mun ce a dauki kowanne irin mataki na shari’a da ya kamata akan wadanda suka yi wan nan aika-aika.

AMMA ABUN MAMAKI… Na fahimci ran wannan karamar yarinyar ya fi rayukan al’umma da dama a arewacin Nijeriya.

Dalilina na fadin haka kuwa tun daga farkon shekarar da ta gabata zuwa yau ban san adadin magidanta da matan aure da kananan yara da aka yiwa irin wannan kisan gillar ba.

Amma ko a labarun gidan rediyo baza ka taba ji ba. Amma abin mamaki yau gashi maganar kashe Haneefa har fadar shugaban kasa sun tanka.

Minista Pantami har gaisuwa saida ya zo. Uwargidan shugaban kasa Buhari ita ma saida ta yi magana.

Mai Martaba Sunusi ll ya tanka. Da sauran kungiyoyin kare hakkin Dan Adam .

Abin nufi a nan yaushe za a tanka ns sauran marayun da ake kashe masu iyaye? Yaushe za a tanka sauran matan da ake kashe masu mazaje?

Yaushe sauran al’ummar da kashe-kashe ya shafa za su samu irin wannan gata da aka yi wa iyayen Haneefa?

A karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna kadai mun sha mu wayi gari mu ji an shiga kauye an kashe akalla magidanta sama da goma, wani lokacin ashirin, kai ko a kwanan nan an kashe mutum sama da arba’in a rana guda, kuma a karamar hukumar Giwa.

Ku sani, su ma irin rayuwar Haneefa gare su, ko an yafe ta sune don suna zaune a kauyaku?

Wallahi Allah ba zai bar ku ba matukar ba za ku yi adalci ba akan rayuwar al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button