News

BIDIYO: Jawabin Makashin Hanifa Abubakar Yayin Da Aka Gufanar Dashi A Gaban Kotu Dan Fara Sauraren Shari’a

Jawabin Makashin Hanifa Abubakar Yayin Da Aka Gufanar Dashi A Gaban Kotu Dan Fara Sauraren Shari’a

Yadda Aka Gurfanar Da Abdulmalik Muhammad Tanko, Da Hashimu Isyaku, Da Fatima Jibrin Musa Da Ake Zargi Da Kisan Hanifa Abubakar Yar Shekara 5 A Gaban Kotu.

Hakika Labarin kisan nata yayi matukar daukar hankalin yan Nigeria Dama Kasashen Waje.

Lauyan Gwamnati Kuma Mai Shari’a Ya Dage Sairaren Karar Har Ziwa biyu ga watan fabirairu Mai Gabatowa.

Kamar Yadda Zaku Gani Acikin Bidiyon Nan Dake Kasa.

“Na same ta a gida lokacin tana bacci kusan ƙarfe 11:00 na dare. Na gama shan shayi na, sai na tashe ta daga bacci.

Na zuba ragowar shayin a cikin robar madarar yara BOBO, na zuba gubar ɓera a ciki.”

“Na faɗa mata zan kaita gidan kawunta ne, kuma akan hanya ne na bata gubar kuma ta sha, daga nan sai muka shiga ɗaya daga cikin reshen makarantar mu, saboda muna da rassa biyu.”

“Na shiga tare da ita bayan na faɗa mata zan ɗauki wani abu ne a ciki. Ta amince ta shiga kuma anan ne ta ƙarisa mutuwa.” Cewar Abdulmalik Tanko makashin HANEEFAH

Tabbas Wannan Rashin Imanin Da Akai Amfani Dashi Wajen Hallaka Wannan Kankanuwar Yarinyar Hanifa.

Ya Matukar Sosa Ran Al’umma Musamman Ma A Shafukan Sada Zumuntar Twitter.

Inda Yan Nigeria Suka Shiga Wallafa Ra’ayoyinsu Akai Tare Da Yin Kira Ga Mahukunta Da Su Gaggauta Zartar da Hukunci Ga Wanda Ake Zirgi Tunda Ya Amsa Laifin Sa.

Ga Bidiyon Nan Ku Kalla

https://youtu.be/2PVl6WcKB7E

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button