News

BIDIYO: Jerin Yara Goma Da Aka Sace Tare Da Yi Musu Kisan Gilla A Nigeria Rahoton Hanifa Shi Ya Tada Binciken Nan

Innalillahi wa inna ilaihi raju’un Kamar Yadda Zaku Gani Cikin Bidiyon Dake Kasa jerin wadansu yara goma da akaiwa kisan gilla a nigeria.

Tun bayan sace hanifa tare da kasheta da wani malamin makarantar su yai, mutane keta yin kiraye kiraye da a gaggauta daukar matakin da ya dace akan makashin nata.

Duba da yadda sace sacen kana nan yara da cin zarafin su ya zama tamkar ruwan dare a nigeria.

Yawaitar cin zarafin yara kanana a nigeria na dada yin tsamari kama daga sacewa fyade garkuwa sayarwa ga wasu iyayen da basa haihuwa dakuma kisan gilla.

Babban abin bakin cikinma shine, yaran na fuskantar hakan daga wadanda aka aminta dasu. Kama daga makota yan uwa malamai da dai sauran su.

Acikin bidiyon da zaku saurara zakuji rahotannin yara goma da aka tabaiwa kisan gilla a nigeria lamarin da ya jefa iyayen su cikin mummunan yanayi.

Anan muke addu’ar Allah ya kawo mana karshen wannan bala’i yajikan musulmai amin summa amin

https://youtu.be/bWVCLezYens

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button