News

BIDIYO: Fusatattun Matasa A Borno Sun Kona Postocin Mawaki Davido’s A Gaba Daya Fadin Jahar Borno, Sun Nemi Ya Fito Ya Nemi Gafara Kan Bidiyon Kiɗa A Masallaci

BIDIYO: Fusatattun Matasa A Borno Sun Kona Postocin Mawaki Davido’s A Gaba Daya Fadin Jahar Borno, Sun Nemi Ya Fito Ya Nemi Gafara Kan Bidiyon Kiɗa A Masallaci

Davido ya wallafa bidiyon mai tsawon dakika 45 na sabuwar wakar Logos Olori, ‘Jaye Lo,’ a shafin Twitter a ranar Juma’a, don tallata wakar.

Wasu matasa a ranar Talata sun Kona fostar shahararren mawakin nan, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido a Maiduguri, babban birnin jihar Borno don nuna fushin Su kan bidiyon wakar wanda Ya Jawo takaddama da Ya Wallafa kwanan nan a shafinsa na Twitter.

Sai dai bidiyon ya haifar da ce-ce-ku-ce yayin da Musulmi da dama ciki har da Bashir Ahmad, tsohon mai taimaka wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, suka nuna wa mawakin fushin su akai.

Masu sukar sun bayyana bidiyon wakar da ke nuna wasu mazan suna sallah da rawa a gaban wani masallaci a matsayin rashin mutunci.

Sun kuma nemi Davido ya bai wa magoya bayan sa Musulmi hakuri.

Sai dai a ranar Talata ne matasan suka fantsama kan titunan Maiduguri, babban birnin jihar Borno domin nuna fusshin su kan bidiyon nan da ya shahara da ake cece-kuce a kansa.

A wani bidiyo da ya yi yawo a shafukan sada zumunta, wanda Sarkin Musulmi (@Sarki_sultan) ya wallafa, an ga wasu matasa a Maiduguri sun kona fostar mawakin tare da neman mawakin da ya nemi ya bai wa al’ummar Musulmi hakuri.

Gadai Bidiyon Ku Kalla

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button