Politics

BIDIYO: Idan Na Ci Zabe Wallahi Saina Sayar wa Da ‘Yan kasuwa Duka Matatun Mai Na Kasa – Atiku

BIDIYO: Idan Na Ci Zabe Wallahi Saina Sayar wa Da ‘Yan kasuwa Duka Matatun Mai Na Kasa – Atiku

“Matsayina akan wannan ba wani sabon abu ba ne, na riga na fada shekarun baya da suka wuce, sayar da su zan yi.”

Dan takarar shugaban kasa karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Atiku Abubakar ya ce, idan har suka kafa gwamnati, zai cefanan da matatun man fetur din Najeriya gaba daya ga ‘yan kasuwa.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka yayin wata ziyara da ya kai Washington.

“Matsayina akan wannan ba wani sabon abu ba ne, na riga na fada shekarun baya da suka wuce, sayar da su zan yi.

“Domin idan ka ba ‘yan kasuwa, za su fi aiwatar da wadannan kamfanoni.” Atiku ya ce a hira da suka yi da shugaban Sashen Hausa na VOA, Aliyu Mustapha Sokoto.

Dangane da batun matsalar satar mai a kudancin Najeriya, Atiku, wanda ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa a tsakanin shekarun 1999-2007, ya ce idan suka kafa gwamnati, za su yi amfani da iko da suke da shi wajen tunkarar wannan matsalar.

“Wannan matsala ce ta daban wacce tilas mu ga yadda za mu yi amfani da karfin gwamnati mu tsayar da wannan, domin akwai hadin kai kwarai da gaske daga ma’aikatan NNPC da ma’aitakan tsaro da aka ba su hakkin kula da hanyoyi ko kuma bututan mai da ake shimfidawa.”

Najeriya na da matatun mai hudu a Kaduna, Warri da Fatakwal, wadanda ba sa aiki yadda ya kamata saboda gyare-gyare da suke bukata.

Hakan ya sa mafi akasarin tacaccen man fetur da ake amfani da shi a kasar, daga kasashen ketare ake shiga da shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button