News

BIDIYO: Innalillahi.. Mutum 51 Ne Suka Mutu Sakamakon Wannan Ambaliyar Da Tafaru A Jahar Jigawa

BIDIYO: Innalillahi.. Mutum 51 Ne Suka Mutu Sakamakon Wannan Ambaliyar Da Tafaru A Jahar Jigawa

Mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Jigawa sun kai 51 da kuma daidaita da dama.

Babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA, Sani Yusuf ne ya bayyana wa gidan talabijin na Channels afkuwar hakan.

A cewarsa, mutum sama da 2,051 ambaliyar ta daidaita a kauyen Karnaya da ke Dutse, babban birnin jihar.

Ya ce gwamnatin jihar na shirin kai uwaye 404 da ‘ya’yansu da suka kai 1,334 zuwa sansanin ‘yan gudun hijira na Warwade, yayin da maza 313 kuma za su ci gaba da zama a wata makarantar firamare da ke kauyen kafin ambaliyar ta ragu.

Babban sakataren ya kara da cewa suna kuma bukatar agaji saboda ambaliyar na ci gaba da shiga kauyuka, inda gadoji da dama suka karye, inda ya gargadi direbobi da su kiyaye yayin tuki.

Ya kuma ce gwamnatin jihar ta mikawa gwamnatin tarayya wnai rahoto, inda take bukatar taimako wajen takaita ambaliyar ruwan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button