News

BIDIYO: Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raju’un Allah Yayiwa Dan Marigayi Sani Abacha Rasuwa A Abuja

BIDIYO: Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raju’un Allah Yayiwa Dan Marigayi Sani Abacha Rasuwa A Abuja

Ɗan Sani Abacha ya rasu

Abdullahi Abacha, wanda shi ne ɗa na biyun-ƙarshe ga marigayi tsohon shugaban mulkin sojan Nijeriya , Sani Abacha, ya rasu yana da shekaru 36 a duniya.

Iyalin Abacha sun tabbatar wa DAILY NIGERIAN rasuwar a yau Asabar, inda suka ce Abdullahi ya rasu ne cikin barci a a gidansu da ke titin Nelson Mandela a Abuja.

“A daren jiya fa lafiyar sa kalaunya kwanta, amma yau da safe sai gawarsa a ka samu. Ya rasu cikin kwanciyar hankali a cikin barcinsa,” in ji wata majiya daga iyalin Abacha.

DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa za’ayi Jana’izar sa da misalin karfe 4 na yamma a babban masallacin kasa dake Abuja a yau Asabar.

An haife shi a shekarar 1987, marigayin yana daya daga cikin yara tara da marigayi shugaban soji ya bari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button