News

BIDIYO: Innalillahi wa inna ilaihir raju’un Yadda Wannan Budurwa Ta Wayi Gari Taga Jikinta Na Kumbura

BIDIYO: Innalillahi wa inna ilaihir raju’un Yadda Wannan Budurwa Ta Wayi Gari Taga Jikinta Na Kumbura

Ana Neman Taimako domin ceto Rayuwar wannan baiwar Allah daga halin da take ciki.

Wannan yarinyar da kuka gani a hoton nan haka kawai ta wayi gari taga jikin ta na kumbura tafin hannun ta yayi baƙiƙƙirin da ƙafafuwan ta, ta shafe tsawon watanni biyar ana nema mata magani na gargajiya saboda ciwon ya yi kama da cuta kamar na masu jinnu.

Bata iya tsugunnawa ta yi bayan gida balle fitsari sai dai ta yi su a tsaye, daga ƙarshe ma tafiyar da takeyi ya gagara Dan haka ta koma yin rarrafe da gwiyawun hannunta wanda yanzu haka sun yi marurai suna zubda mugunya.

Ganin an gagara Gane ciwon da ya ke tattare da ita ya sa mai maganin ya turasu asibitin 44 da ke Kaduna, domin a binciki abinda ya ke damun ta, nan aka sayar da keken dinkin ta suka yi kuɗin mota su ka je, an rubuta musu test da scanning duk sun saya tare da magunguna don haka tun ajiyan kuɗin da suka tafi dashi ya ƙare, sai dai wani test guda da aka rubuta musu na naira dubu arba’in wanda ya gagare su, ga kuɗin gado wanda duk rana dubu biyar ne, ga kuɗin abinci, dan Allah ƴan uwa ku taimaka mai biyar, mai goma.

Ga duk Mai buƙatar taimakawa Yana iya tuntuɓir wannan numbar +2348107125536
Inda zai Sami mahaifiyar yarinyar Kai tsaye.

Account number: 1513604714
Branch :Access Bank
Account name:Maryam Idris.
Lambar waya. 08107125536

A domin Hakane ake Neman da al’ummar Musulmi su Cigaba da yada wannan rubutun ta Hanyar turawa Zuwa manjaharsu na Fesbuk da Kuma wasu Zauruka, Kan taimakawa wannan baiwar Allah.

Ubangiji Allah Kabata Lafiya Amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button