News

BIDIYO: Kotu Ta Wanke Matar Abdulmalik Tanko Jamila Sani Wanda Ake Zargi Da Kashe Haneefa Abubakar

Hanifa: Kotu ta wanke matar Abdulmalik Tanko

Kotun Majistire mai mai lamba 12 da ke zaman ta a gidan Murtala, Jihar Kano, ta wanke Jamila Sani, matar Abdulmalik Tanko, wanda a ke zargi da garkuwa da kuma kashe Hanifa Abubakar.

A jiya ne dai Babbar Kotun Jiha mai lamba 5, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Usman Na-abba, ta gayyaci Jamila domin ta bada shaida a kan Tanko, bayan da ya musanta cewa shi ya kashe Hanifa.

A yau ne a ka gurfanar da Jamila a Kotun Majistare ɗin, bayan da Tanko ya ce a gidansa ya ajiye ta, a hannun matarsa.

Da ya ke yanke hukunci a kan tuhumar da a ke mata, alƙalin kotun, Muhammad Jibril ya wanke Jamila bisa hujjar cewa babu hannun ta a ciki.

Alƙalin ya ce hasali ma, ƙarya Tanko ya yi wa matar tasa da cewa Hanifa ƴar gidan wata malama ce mai aiki a makarantar sa da ta samu aiki a Saudiyya, shine ta je Abuja domin kammala shirin tafiya Saudiyan.

Da ga ƙarshe alƙalin ya wanke ta ya kuma bada umarnin a sake ta sabo da ba a same ta da hannu a cikin laifin ba.

https://youtu.be/lUwm0j7w1NE

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button