News

BIDIYO: Muna Da Yan Mata Kala Kala A Wajejen Mu Don Haka Adaina Cewa Munayiwa Mata Fyade- Bello Turji

Fitaccen Kasurgumin Dan Fashin Dajin Nan Wato Bello Turji Ya Musanta Zargin Da Ake Masa Na Aikata Fyade,

Bello Turji Ya Musanta Hakan Ne, Acikin Wata Tattaunawa Da Sukai Da Jaridar Aminiya.

Inda Yace Su Fulani Sun Dauki Makamai Ne Dan Kawai Hakan Ya Zamar Musu Dole Ne.

Inda Ya Kara Da Cewa Shi Sam Baya Aikata Fyade, Domin A Inda Yake Akwai Mata Bijij.

Ya Kuma Yi Misali Da Jahar Kano, Inda Yace Yanzu Duk Matan Dake Kano Wadanda Akaiwa Fyade Kenan Shi Yayi Musu?

Kamar Yadda Zakuji Acikin Bidiyon Dake Kasa, Jaridar RFI hausa Ta Rawaito Cewa.

Kiddidiga  ta nuna cewa yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira dubu 780 a jihar Zamfara ta arewa maso yammacin kasar kawai.

A wata ganawa da ya yi da jaridar ‘Aminiya’, kasurgumin dan bindigar nan mai suna Bello Turji, wanda ake zargi da yawancin ta’asar da ake aikatawa a yankin arewa maso yammacin kasar ya musanta laifukan da ake zarginsa da aikatawa.

Turji ya ce kowa na iya fadin abin da ya ga dama, amma abin da ya sani shine, shi ba ya fyade, yana mai cewa akwai mata a inda yake.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button