Religion

BIDIYOYIN: Jerin Malaman Da Suka Sha Zagi A Dandalin Sada Zumunta Saboda Sun Bada Fatawa

Jerin Malaman Addinin Da Suka Sha Zagi A Shafukan Sada Zumunta Kan Fatawar Da Suka Bada

1- Sheikh Abduljabbar Kabara akan FAHIMTA.
Kowa yasan abinda yake faruwa akan malam masu hujja sunada hujja wadanda basuda ita kuma sai zagi, dayawa kamar kiris ake jira.

2- Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar akan SAKIN AURE A FILM.
Shima malam yayi wannan maganar ne tare da hujja wadanda suka fahimta sun fahimta wadanda basu fahimta ba sai zagi da cin mutunci.

3- Sheikh bin Usman akan CRYPTO.
Shima yayi magana akan yan crypto, in ba zaku manta ba babu irin zagin da ba’ayiwa malam ba akan wannan.

4- Sheikh Abubakar Mukhtar Yola POS.
Yayi magana akan haramcin Sana’ar POS amma wadanda basuda tunani sai suka dinga zagin malam, bayan shi da hujja yayi fatawarsa.

5- Sheikh Dr isa Ali fantami AKAN TSOHUWAR Akida. Lokacin da akace an bawa fantami minister aka dinga fito da tsofaffin videos dinsa ana zaginsa dasu, har yanzu masu zafin akida suna zagin malam, sai ka rasa to mene amfanin hakan?

6- Sheikh Ibrahim Maqari KAN HARAMCIN BIYAN KUDIN FANSA. Lokacin da malam yayi wannan maganar babu irin zagin da ba’ayi masa, wasu har addu’a suke Allah yasa a kama wani nasa saboda kawai bambancin akida

7-Albanin Gombe AKAN MATAN DUNIYA DANA ALJANNA. lokacin da yake magana akan dadin matan aljanna yayi wata magana wadda yake bayanin matan duniya basu kai na aljanna ba, ga video din nan dai a kasa

8- MALAM IBRAHIM KHALIL AKAN JIN WAƘA,
kwanaki kadan da suka wuce malam yayi magana akan jin waƙa kuma ya kawo hujja amma hakan yasa aka dinga zagin malam.

 

9- SHEKH ABDALLAH GADON KAYA AKAN MA’AIKATAN LAFIYA,
Basai nayi bayani ba kowa yasan yadda aka dinga zagin malam akan wannan batu kuma malam gaskiya ya fada duk wanda yake garin nan yasan abinda malam ya fada gaskiya ne.

10- MALAM AMINU IBRAHIM DAURAWA yayi magana akan mumin gaban mace, kuma malam yayi maganar ne domin nuna rashin dadi ga aikata zina, amma sai wasu maza da mata musamman mata yan iska suka dinga zagin malam saboda ya fadi haka, kuma duk a malamai babu wanda yake kare martabar mata kamar malam Aminu Ibrahim daurawa.

Indai za’a tafi a haka wlh babu abinda hakan zai amfanemu dashi sai kiyayya da juna. babu dama wani malami me wata akida wadda ba irin tamu ba ya fadi abu wanda ya saba da ra’ayinmu sai mu fara zagi da cin mutunci,

wannan babu inda zai kaimu face cusa mana kiyayyar juna saboda kare akida,

Ni duk malamin da yayi magana in bata yimin dadi ba bazan Zageshi ba, ni na bawa malamai yadda dari bisa dari, nasan malami bazan fadi magana domin san zuciyarsa ba dole akwai abinda yakeso ya isar kokuma abinda yake nufi daban abinda masu sauraro suke nufi daban.

 

Allah yasa mu dace ya bamu lafiya da tsawon rai 🙏

Malam Musa Rafinkuka
6/3/2022

https://youtu.be/uMkYX5AtBrM

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button