News

BIDIYO: Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Yi Gagarumar Nasara Kan ‘Yan Bindiga A Yankin Chikun Dake Jihar Kaduna, Inda Aka Kama Guda 50 A Raye

BIDIYO: Rundunar Sojojin Nijeriya Ta Yi Gagarumar Nasara Kan ‘Yan Bindiga A Yankin Chikun Dake Jihar Kaduna, Inda Aka Kama Guda 50 A Raye

Kamar Yadda Zaku Gani Cikin Bidiyon Dake Kasa, An Hango Rundunar Sojojin Na Yunkurin Dora Yan Garkuwa Da Mutanen Da Ta Kama A Cikin Mota Hilos.

Kamar Yadda Bidiyon Ke Cigaba Da Yaduwa Musamman Ma A Shafukan Sada Zumuntar Zamani.

Inda Mutane Ke Wallafa Tare Da Jinjinawa Jami’an Sojojin Nigeria Tare Da Bukatar Acigaba Da Yi Musu Addu’a Musamman Ma Acikin Wannan Wata Namu Mai Girma.

Jahar Kaduna Na Daya Daga Cikin Jahohin Da Suke Shan Fama Da Hare Haren Yan Garkuwa Da Mutane Lamarin Da Ya Kara Kamari A Yan Kwanakin Nan.

Lamarin Garkuwa Da Mutane Domin Amsar Kudin Fansa, Na Cigaba Da Ciwa Al’umma Tuwo A Kwarya Musamman Ma Al’ummar Yankin Arewacin Nigeria.

Inda Al’umma Ke Ganin Gazawar Gwamnati Akan Samar Da Tsaro Dakuma Kawo Karshen Yan Ta’addan Kamar Yadda Ta Alkawuranta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button