BIDIYO: Yadda Ambaliyar Ruwa Ke Kwashe Motoci Tare Da Rushe Gidaje A Birnin Lagos

Wani Rahoto Da Muke Samu Yanzu-Yanzu Na Cewa, Ambaliyar ruwa na neman shafe birnin Legas da ke Najeriya.

Yayin da mazauna Legas da ke Najeriya, ke ci gaba da fuskantar matsalar ambaliyar ruwa kowacce shekara.

musamman a watannin Maris zuwa Nuwamba, a ‘yan shekarun nan yankin na fama da mummunan matsalar ambaliyar ruwa.

Wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da hukumomi a Najeriya ke ci gaba da gargadin aukuwar wata ambaliyar nan da dan lokaci kadan.

Haka zalika masana na ganin cewa birnin na Legas ya fara nutsewa a cikin ruwa, sakamakon matsalar dumamar yanayi.

Latsa Bidiyon Nan domin Kallon rahoton Shamsiyya Haruna.

Click Here To Drop Your Comment