News

BIDIYO: Yadda Wani Ragon Sallah Ya Tsere Kafin A Yanka Shi Ya Hau Ginin Beni Me Hawa uku Yaki Ya Sauko

BIDIYO: Yadda Wani Ragon Sallah Ya Tsere Kafin A Yanka Shi Ya Hau Ginin Beni Me Hawa uku Yaki Ya Sauko

Wani abun al’ajabi daya faru a safiyar yau shine, yadda aka wayi gari da ganin wani ragon Sallah layya ana dab da yanka shi ya tsere yahau wani ginin beni me hawa 3 a jahar Lagos.

Lamarin ya faru a safiyar yau bayan sallah idi anyi iya kokari aga a sauke ragon amma yaki saukowa.

Kamar Yadda zaku kalli acikin bidiyon dake kasa, ragon dai ya tsere ne bayan yaga anata yanka yan uwan sa raguna.

Lamarin da yasa yace kafa mai naci ban baki ba, yai sauri ya haye saman wani bene mai hawa uku.

Daruruwan mutane ne suka taru domin ganin an sakko da ragon lafiya batare da ya samu wata matsala ba.

Ga bidiyon nan ku kalla::

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button