News

BIDIYO: Yadda Wata Mahaifiya Ke Shelan Neman Wanda Zai Kashe Mata Dan Cikinta Usman Ta Biyashi

BIDIYO: Yadda Wata Mahaifiya Ke Shelan Neman Wanda Zai Kashe Mata Dan Cikinta Usman Ta Biyashi

Mahaifiya a garin Zariya tayi Shelan Neman Wanda zai Kashe mata Dan cikin ta

Daga Wakilinmu

Wata mahaifiya a garin Zariya Jihar Kaduna, ta Shaidawa Jami’an tsaro na ‘Yan Sanda Shiyyan Zariya cewa, da Allah Zai kawo Wani mutum dan albarka da zai Zama Silar mutuwar Dan cikinta da Sai ta kwana tana Masa addu’ar Allah ya biya shi, ita a nufinta akashe kawai kota halin Kaka Saboda yafi karfinta, kullum shikenan hadata rigima da al’umman gari.

Usman Shine Sunan Matashin, Wanda mahaifiyarsa ta gaji da ganinsa a doron Kasa, Saboda irin rigimar da yake dauko Mata, yau Shine ya Sari wancan gobe ya Soke wancan.

Hakan ya Kara bude Wani Sabon fai-faine, a dalilin yadda Matashin ya Sossoke Wani Dan uwansa Matashin Mai kimanin Shekara 29 da wuka, har sai da lamarin ya Kai ga ‘Yan Sanda, “Inda aka bukaci mahaifiyar Wanda ya aikata wannan mummunar ta’asar data bayyana a gaban hukuma duba ga yadda Shi Dan nata yayi na Kare.

Wakilin ALFIJIR HAUSA ya bibiyar lamarin ya Kuma tabbatar da wannan kalamin da mahaifiyar Usman din tayi, Mahaifiyar take Shaidawa Jami’an tsaro ita Bata San inda Dan nata ya shiga ba amsar data baiwa Jami’an tsaron kenan bayan tambayarta da Jami’an tsaron Suka Yi ko ta Sana inda dan nata ya Shiga.

Bisani yadda Jami’an tsaron Suke sintirin farautar Usman din a domin ya gurfana gaban hukuma Kan irin ta’asar da yayi, a takaice dai Saboda irin gundurar da mahaifiyar tayi da Dan nata har ya kai ga ta Shaidawa Jami’an tsaro cewa, ita kawai mummunar ajalin Dan nata take jira Allah ya nuna Mata tun tana Raye.

Shidai Matashi Usman Haifaffen Tudun wadan Zariya ne, dan Wani Shiyya da ake Kira da gangaren kwadin Usman ya addabi Al’umma kullum Sai ya jangwamoma mahaifiyarsa rigima, bakin ciki yau daban ta gobe daban.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button