News

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un; Ku Kalli Yadda Akayi jana’izar mutum 13 da ‘yan fashin daji suka kashe a Jihar Taraba

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un; Ku Kalli Yadda Akayi jana’izar mutum 13 da ‘yan fashin daji suka kashe a Jihar Taraba

Mutum aƙalla 13 aka kashe sakamakon harin da ‘yan fashin daji suka kai a ƙauyen Karekuka na Jihar Taraba da ke tsakiyar Najeriya da tsakar ranar Juma’a.

Kazalika, an jikkata mutanen da ba a san adadinsu ba a harin waɗanda ke jinya yanzu haka a Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke birnin Jalingo, kamar yadda kakakin ‘yan sanda na Taraba ya shaida wa BBC Hausa.

Tuni aka yi jana’izar mutanen a garin da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, akasarinsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

‘Yan sanda sun ce tun farko mutanen garin ne suka kama ɗaya daga cikin ‘yan fashin bayan wani hari da suka kai kuma suka kashe shi, inda su kuma suka kashe mutum 13 a harin ramuwar gayya.

Sai dai wasu rahotanni na cewa ‘yan bindigar sun sake yi wa Garin Gidado tsinke a safiyar yau Asabar amma sun tarar ba mutane a garin.

SP Abdullhi Usman ya ce an tura jami’an tsaro yankin don kwashe gawarwakin mutanen bayan harin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button