News

Innalillahi bidiyon Yadda Aka Cafke wani matashi yana yiwa wata mahaukaciya fyade a Neja

Innalillahi bidiyon Yadda Aka Cafke wani matashi yana yiwa wata mahaukaciya fyade a Neja

Ƴan sanda sun cafke wani matashi mai suna Haruna Musa, mai shekara 21 a duniya, wanda aka kama dumu-dumu yana yin fyade ga wata mahaukaciya a Angwan Gwari Kwamba cikin ƙaramar hukumar Suleja, ta jihat Neja a daren ranar Talata.

A wani bidiyo da jaridar Daily Trust ta samo, an jiyo Musa yana cewa bai riga da ya shiga matar ba kafin ta fara ihu wanda ya fargar da mutane. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Matashin ya bayyana abinda yaja hankalin sa wurin ƙoƙarin yiwa mahaukaciyar fyade Musa, wanda aka same shi ƙullin tabar wiwi, ya ɗora alhakin abinda ya aikata akan shaye-shaye da kuma tsinuwa daga ƙauyen shi. Ya ƙara da cewa halin tsirarar da matar take ciki shine abinda ya ja hankalin shi zuwa gare ta.

Ya bayyana cewa: Idan da ba don jami’an tsaro ba da ƙila sai na sadu da ita. Ban san abinda ya shige ni ba. Ku yafe min. Shekara ta 21 kawai a duniya. Ina da abubuwa da dama a zuciyata.

Matsalolina sun fi ni ƙarfi. Bani da kowa wanda zai taimaka min. A Najeriya matsalar fyade na daɗa ƙaruwa musamman akan ƙananan yara maza da mata.

Yara da yawa na fuskantar matsalar fyade idan sun fito daga gidajen iyayen su. Ba ƙananan yara kaɗai ba, har ƴanmata da matan aure ba su tsira ba daga wannan babbar matsalar da ake fama da ita a ƙasar.

https://youtu.be/HLRVkc0HDac

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button