News

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un;! Wasu Matasa Hudu Sun Gamu Da Ajalinsu A Hanyar Su Ta Zuwa Daurin Auren Abokin Su

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un;! Wasu Matasa Hudu Sun Gamu Da Ajalinsu A Hanyar Su Ta Zuwa Daurin Auren Abokin Su

Hadarin Mota Ya Yi Silar Mutuwar Wasu Matasa Hudu A Hanyar Zuwa Auren Abokinsu A Katsina.

Engr. Danbaba Foundation na mika sakon ta’aziya ga iyalan ‘yan uwa da abokan arziki na rashin nagartattun Matasa da karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna ta yi sakamakon hadarin mota.

Hadarin mota ya rutsa da matasan ne akan hanyar su ta zuwa Katsina domin daurin auren abokinsu Aliyu Osama wanda ya gudana a yau Asabar 13/08/2022.

Cikin matasan da Allah ya karbi rayuwarsu sun hada da Babban Aboki na Engr. Danbaba, wato Malam Shafi’u Adamu wanda ya kasance hazikin matashi mai addini da son cigaban al’umma, sannan akwai Samaila Passion, da Alh. Umaru da Sule Unguwan Rimi.

Hakika wadannan matasa suna bukatar addu’o’in ‘yan uwa musulmi baki daya.

Allah ya jikansu, Allah Ya yi musu rahama, Allah, ya sanya su gidan Aljannah. Allah ya baiwa iyalansu hakuri na rashinsu.

Daga Engr. Danbaba
A madadin ‘Danbaba Foundation’.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button