News

BIDIYO: Yan Boko Haram Sunyiwa Wadanda Suka Kubutar Daga Gidan Yari Wa’azi Tare Da Raba Musu Kudin Mota

BIDIYO: Yan Boko Haram Sunyiwa Wadanda Suka Kubutar Daga Gidan Yari Wa’azi Tare Da Raba Musu Kudin Mota

(ISWAP) ta dauki nauyin fasa gidan yarin Kuje

Rahotanni sun ce sai da ‘yan ta’addan suka tsaya suka yi wa’azi kafin su kubutar da mutanensu Baya ga wa’azi, an rabawa wadanda aka kubutar kudi domin su hau mota, su sulale daga Abuja

Bayan ‘yan ta’addan (ISWAP) kutsa kai gidan yarin, tare da fadawa wadanda ke ciki cewa duk mai niyyar fita zai iya sulalewa.

Wata majiya ta shaida cewa ‘yan ta’addan na kungiyar ISWAP ba su tursasawa kowa tafiya ba, amma sun fadawa masu niyyar sulalewa su hadu da su a waje.

Da aka hadu a wajen gidan yarin na birnin tarayya Abuja, akwai motoci da ‘yan ta’addan suka tanada domin tsofaffin mayakan Boko Haram da ke zaman kaso.

Bayan sun shiga motocin, sai suka raba masu kudi da za su yi zirga-zirga, har su batar da sahu.

Jaridar legit ta ce ‘yan ta’addan sun yi wa wadanda ba ‘yan kungiyarsu ba ne barazanar cewa ka da su shiga motocinsu, an nuna za a kashe duk wanda ya shiga motocin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button