Religion

DIRAMA: Bidiyo Rashin samun tafiya Aikin Hajji Bakano Zai gudanar da aiki Hajji a Filin Jirgi

Rashin samun tafiya Aikin Hajji Bakano Zai gudanar da aiki Hajji a Filin Jirgi

Daga Bilyamin Ahmad Magami

“Wani Maniyyaci Daga Jahar Kano Wanda Bai Samu Shiga Rukunin Karshe Da Jirgi Ya Đauka Ba, Ya Ayyana Cewa Shirye Yake Tsaff Domin Gabatar Da Aikin Ibadar Hajjin Shi A Sansanin Alhazzai Na Jahar Kano.

“Malam Jibrin Abdu Daga Garin Gezawa Ya Zama Abun Kallo Bayan An Gan Shi Cikin Shigar Farin Harami Kuma Ya Bayyana Cewa Tuni Ya Fara Aikin Hajjinsa a Sansanin Alhazzai Dake Jahar.

“Ya ce: Ya Siyar Da Gonarsa Domin Ya Samu Damar Zuwa Sauke Farali A Shekarar Bana, “Amma Wasu Gurɓatattun Jagorori Suka Hana Mafarkinsa cika,” Duk Da Ya Rungumi Hakan A Matsayin ƙaddara Ya San Da Cewa Haka Allah ya tsara.

Bayan Nan Ya Yiwa Sauran ‘Yam Uwansa Mahajjata Huduba Da Wa’azi Akan Kada Su Samu Damuwa Ko Wani Abu Makamancin Haka, Su Đauka Kawai Haka Allah Ya Kaddarta.”

Ga Bidiyon Kusha Kallo

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button