BIDIYO: Yanzu-Yanzu Gwamnati Ta Saka Dokar Hana Fita A Jahar Sokoto Ta Tsawon Awa 24

Gwamnatin Jihar Sokoto ta saka dokar hana fita ta tsawon awa 24 a jihar sakamakon zanga-zangar da wasu mazauna jihar suka gudanar a yau Asabar.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta wallafa a shafinta na Facebook ta ce dokar za ta fara aiki nan take.

An ɗauki matakin ne “saboda dawo da doka da oda a birnin Sokoto da jihar baki ɗaya”, a cewar sanarwar.

Masu zanga-zangar na nemanjami’an tsaro su saki mutanen da suka kama da ake zargi da kisan matashiyarda ke karatu a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, wadda suka zarga da zagin Annabi Muhammadu (SWA).

Ku Kalli Bidiyon Anan

Click Here To Drop Your Comment