News

BIDIYO: Yanzu-Yanzu Yan Sanda Sun Kama Abdullahi Yar Dubu Wanda Yaje Kan Kabari Ya Zagi Mahaifiyarta

BIDIYO: Yan Sanda Sun Kama Abdullahi Yar Dubu Wanda Yaje Kan Kabari Ya Zagi Mahaifiyarta

Tun bayan wani dan gajeren bidiyo da ya fita a shafukan sadaa zumunta.

Wanda acikin bidiyon aka hango wani dan daudu akan kabarin wata abokiyar fadan sa yana zagin mahaifiyar ta dake kwance acikin kabarin.

Lamarin da yasa Al’umma ke kiranye ga gwamnati tare da hukuma data gaggauta kama shi domin abinda ya aikata ya girmama.

Tare da yin kira ga gwamnati da a gaggauta kulle shafin tiktok a nigeria.

A yanzu haka labarin dake iske mu shine Rundunar yan sanda reshen jahar kano ta sanar da kame wannan matashi kamar yadda nasir salisu zango ya wallafa a shafin sa na sada zumunta cewa.

Ga Bidiyon Zagin Da Yayi

https://youtu.be/k58a42eVWuY

Ƴansanda a Kano sun cafke wani matashi ɗan hamsin mai suna Abdullahi Ƴar Dubu mazaunin unguwar Sharaɗa, wanda yaje maƙabartar Ɗandolo ya tsaya a kan kabarin wata baiwar Allah yana ƙunduma ashariya, sakamakon saɓani da suka samu da ƴarta.

Ƙarin bayani zai zo nan gaba.

Abdullahi Yar dubu ya shiga hannun’yansandan sharada, kuma yanzu haka an tusa keyar sa zuwa shalkwatar yansanda dake Bompai

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button