Politics

BIDIYO: Zan Kwatanta Shugabanci Irin Na Sahabban Manzon Allah S.A.W Idan Allah Ya Ba Ni Mulkin Nijeriya, Cewar Bola Tinubu

Zan Kwatanta Shugabanci Irin Na Sahabban Manzon Allah S.A.W Idan Allah Ya Ba Ni Mulkin Nijeriya, Cewar Bola Tinubu

Ita siyasa ba wai batu ne na shugabanci ba kawai, babban lamari ne akan sha’anin ilimi da ruhin al’umma da wayewar kan mutane da fahimtarsu da kuma aiwatar da daraja da tsare-tsare kyawawa – Cewar Bola Ahmed Tinubu.

Bola Tinubu yaci gaba da cewa Musulunci ya na koyar da mu kan mu cimma waɗannan ta hanyar da ta dace, waɗanda su ka haɗa da ba da shawara, da samar da mutane taurari abin koyi, da kykkyawan tunani da shugabanci nagari da sauransu. Manufar shugabanci a musulunci shi ne nusarwa da jagorantar al’umma kan ayyuka na kwarai da gujewa munana. Amana, gaskiya, adalci nagartocin musulunci ne da ake aiwatar da su a siyasa. Waɗannan kyawawan halaye daraja ce da ke kai shugaba ko ɗan siyasa ko duk wani bawa zuwa ga Aljanna ranar gobe ƙiyama.

A cikin Al”qur’ani mai girma, Allah maɗaukakin Sarki ya ce: “Sannan kuma mun sanya musu shugabanni a a bayan ƙasa waɗanda za su riƙa jagoranci a bisa umarninmu; sannan kuma mun yi musu wahayi akan aiki na ƙwarai, da kula da Sallah da albishir da kykkyawan sakamako. Su ne bayi masu sadaukarwa a gare mu”. (Qur’an, 21:73).

Dogaro da wannan aya ta Al’qur’ani, za mu fahimci cewa Shugabanci siffa ce ta Allah, shi ne ya ke zaɓar shugaba ba wani mutum ko wasu ƴan kwamiti ba. Rawar da shugaba ya ke takawa a taƙaice ta ke, domin ya nusar ya kuma kafa daular musulunci.

Ya ƙara da cewa Manzon Allah S.A.W ya aiwatar da su waɗannan kyawawan halaye ya kuma zama abin koyi. Wata alama ta ƙarin shaidar shugabanci nagari, a matsayin shugaba na Madina, ya buɗe zauren karɓar shawarwari daga sahabbai (Shura) inda ake tattara shawarwari da ra’ayoyi a yi muhawara a kai a ɗauki duk abin da ya dace a aiwatar.

Tinubu yace matuƙar mun yi nasara a zaɓen 2023 zamu tabbatar mun gida jami’ar musulunci mafi girma a Nahiyar Afrika a Arewacin Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button