News

Bidiyon Tarihin Basaraken Da Ya Tafi Hajji Da Mutum Dubu Sittin 60.000 Ya Ninka Elon Musk Arziki

Basaraken Da Ya Tafi Hajji Da Mutum Dubu Sittin 60.000 Ya Ninka Elon Musk Arziki

Labarin Mansa Musa, Basaraken Afrika da ya Ninka Musk Arziki.

Yayin da Elon Musk ya kasance mutum mafi arziki a duniya a yau, masana tarihi sun ce kudinsa ba komai ba bane idan aka hada shi da Mansa Musa.

Mansa Musa dai basarake ne ‘Dan Afrika kuma yayi rayuwa a karni na 14 wanda masana tarihi suka ce shi ne mutumin da yafi kowa kudi a tarihin duniya.

Sai dai wani babban abu Da Zai Baka Mamaki Da Mansa Musa Shine, duk da wannan kudin, ba komai ne Mansa ya samu ba domin akwai lokacin da ya bayar da buhun zinari aka bashi buhun gishiri daya tak.

Kamar yadda bayanin Bloomberg ya bayyana, manyan masu kudin duniya sune Elon Musk, Bernard Arnault, Jeff Bezos da Gautam Adani.

Rahoton ya nuna cewa Elon Muska yana da tarin dukiya da ta kai $198 biliyan.

Duk da kuwa wannan yawan dukiyar, Musk bai zo ko kusa da Mansa Musa ba, basaraken Afrika da yayi rayuwa a karni na 14 wanda ke da dukiya ta bada mamaki.

A takaice, Musk baya cikin biloniyoyin duniya idan muka duba tarihi, Scmp sun yi ikirarin cewa John D. Rockefeller da Augustus Caesar sun fi shi kudi.

Waye Mansa Musa??

A Mandinka, Mansa na nufin basarake ko shugaba.

Kamar yadda BBC ta bayyana, an haifa Musa Keita wuraren 1280CE yayin sarautar Keita.

An haife shi a gidan sarauta da suka karba karagar mulki a 1312 C3 yayin da ‘dan uwansa Mansa Abu-Bakr yayi watsi da karagar domin wata tafiya a teku.

Ko a lokacin da ya hau kan karagar mulkin, an tabbatar da cewa yana da mashahuriyar dukiya.

Masana tarihi sun ce masarautar Mali a wannan lokacin ita ce inda aka fi samun gwal a duniya kuma take samarwa da samar wa da rabin duniya kamar yadda gidan tarihin birtaniya ya bayyana.

Ya kudin Mansa Musa suke?

Wasu masu kiyasi sun kwatanta azikinkinsa da $400 biliyan zuwa $500 biliyan duk da akwai matukar wahala a yi kiyasin daidai duba da lokacin ana amfani da gwal, gishiri da filaye ne wurin bayyana arziki.

Masana tarihi masu tarin yawa sun sakankance cewa arzikinsa yafi duk duniya.

Ranar da ya bayyana arzikinsa a duniya A matsayinsa na Musulmi, Musa ya fara tafiya zuwa Makka daga 1324 zuwa 1325 wanda yanzu aka ce shi ne tafiya mafi almubazzaranci da wani mahaluki yayi a duniya kamar yadda Magnates Media suka bayyana.

Musa ya tashi da nufin bayyanawa duniya sunansa, kuma tafiyar nan ta nisan kilomita 6,500 ita ce damar da zai yi hakan. BBC ta rahoto cewa basaraken ya bar kasar Mali da mutane 60,000 wadanda suka hada da mata da maza, daga dogarai zuwa matukan rakuma da bayi dauke da jakunkunan danyen gwal.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button