News

Bidiyon Yadda ‘Yan Jagaliyar Siyasar Dan Majalisar Tarayya Daga Jihar Borno, Saleh Satomi Suka Ci Zarafin Wata Matashiya

Yadda ‘Yan Jagaliyar Siyasar Dan Majalisar Tarayya Daga Jihar Borno, Saleh Satomi Suka Ci Zarafin Wata Matashiya

A bidiyon an ga yadda matasa ‘yan bangar siyasar suka din ga dibgawa matashiyar mai suna Fadila Abdulrahman.

Duk da ruwan ashariya bisa kalubalantar dan majalisar da ta yi a siyasance a shafin ta na sada zumunta.

Baya ga dukan da ‘yan jagaliyar suka yi mata sun kuma farfasa wurin da matashiyar take sana’a.

Rahotanni sun nuna cewa tuni dai Gwamna Zulum ya bada umarnin a zakulo matasan da suka ci zarafin matashiyar bisa bambancin ra’ayi na siyasa.

Inda wasu kuma suke yin kira ga hukuma da su gayyato dan majalisar domin wanke kansa daga aika-aikar da ‘yan jagaliyar nasa suka yi.

DAGA Haruna Chizo Germany Ga Bidiyon Anan

https://youtu.be/oClQNdpXj_g

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button