News

Cikin Bidiyo: Yadda Matasa Suka Bankawa Makarantar Su Hanifa Wuta Da Tsakar Daren Litinin

Yadda Matasa Suka Bankawa Makarantar Su Hanifa Wuta Da Tsakar Daren Litinin

Rundunar Yan Sanda A Jahar Kano Dake Arewacin Nigeria Ta Tabbatar Da Afkuwar Lamarin.

Inda Ta Tabbatar Da Cewar Matasan Da Ba’asan Ko Su Waye Ba Sun Bankawa Makarantar Wuta Kamar Yadda Zaku Gani Cikin Bidiyon Dake Kasa.

Tun Bayan Da Aka Gano Gawar Hanifa Acikin Kabarin Da Makashinta Ya Binneta A Harabar Makarantar.

Hakan Ya Fusata Matasa Harma Sukai Yunkurin Kona Makaranatar Amma Yan Sanda Suka Hana.

Sai Dai A Daren Lahadi Ne Aka Samun Rahoton Cewa Wasu Fusattun Matasa Sun Kone Makarantar.

Lamarin Da Yasa Datti Assalafy Yin Martani Akai Inda Yace Hakan Badai Dai Ne Ba.

Wannan hukunci da wasu matasa suka dauka rashin hankali ne ba daidai bane har a tsarin Ubangiji, domin ginin makarantar ba mallakin Abdulmalik bane, na wani bawan Allah ne ya bashi haya.

Makaranta ce wanda take kusa da gidajen mutane bayin Allah, idan ansa wuta babu wanda yake da tabbacin wutar zata tsaya iya makarantar bai shafi gidan mutane ba

Duk wanda yake da hannu a lalata dukiyar wani to ya dauka wa kansa bashi da zai biya da ladansa a ranar Hisabi

Jama’a ya kamata mu kasance al’umma da take da tsari mai kyau da sanin yakamata da kuma bin doka

Allah Ya sauwake Gadai Bidiyon Ku Kalla Anan.

https://youtu.be/n093E564MeA

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button