News

Yadda Fusatattun Matasa Suka Banka Wuta A Makarantar Su Hanifa Abubakar Yarin Da Malamin Su Ya Hallakar

Fusatattun Matasa Sun Cinna Wuta A Makarantar Su Hanifa Abubakar Yarin Da Malamin Su Ya Hallakar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa wasu matasa sun kona makarantar su Hanifa Abubakar.

Yarinyar nan ‘yar shekara biyar da ake zargin mai makarantar ne ya kashe ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa BBC cewa.

“Matasan sun kona makarantar ce da tsakar daren Litinin.

Sai dai ya ce kawo yanzu ba su kama wadanda ake zargi da aikata ta’asar ba.

A makon jiya ne aka gano gawar Hanifa wadda ake zargin mai makarantar Noble Kids School ya sace a ranar 4 ga watan Disambar 2021.

Wannan Matakin Da Matasa Suka Dauka Badai Dai Bane A Cewar Datti Assalafy

Inda Ya Kara Da Cewa “Wannan hukunci da wasu matasa suka dauka rashin hankali ne ba daidai bane har a tsarin Ubangiji, domin ginin makarantar ba mallakin Abdulmalik bane, na wani bawan Allah ne ya bashi haya

Makaranta ce wanda take kusa da gidajen mutane bayin Allah, idan ansa wuta babu wanda yake da tabbacin wutar zata tsaya iya makarantar bai shafi gidan mutane ba

Duk wanda yake da hannu a lalata dukiyar wani to ya dauka wa kansa bashi da zai biya da ladansa a ranar Hisabi

Jama’a ya kamata mu kasance al’umma da take da tsari mai kyau da sanin yakamata da kuma bin doka

Allah Ya sauwake

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button