News

CIKIN BIDIYO: Abin Da Nacewa Hanifa Kafin Na Bata Bobo Da Maganin Bera Tasha Ta Mutu Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un

Abin Da Nacewa Hanifa Kafin Na Bata Bobo Da Maganin Bera Tasha Ta Mutu Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un

“Na same ta a gida lokacin tana bacci kusan ƙarfe 11:00 na dare. Na gama shan shayi na, sai na tashe ta daga bacci. Na zuba ragowar shayin a cikin robar madarar yara BOBO, na zuba gubar ɓera a ciki.”

“Na faɗa mata zan kaita gidan kawunta ne, kuma akan hanya ne na bata gubar kuma ta sha, daga nan sai muka shiga ɗaya daga cikin reshen makarantar mu, saboda muna da rassa biyu.”

“Na shiga tare da ita bayan na faɗa mata zan ɗauki wani abu ne a ciki. Ta amince ta shiga kuma anan ne ta ƙarasa mutuwa.”

“Na binne gawar Hanifa a cikin harabar makarantar saboda ban samu damar neman wani wuri mai tsaro da zan binne ta ba.” Inji Abdulmalik

Haryanzu alumar musulmi Suna jimamin mutuwar hanifa Yar shekara biyar da Shugaban makarantarsu ya kasheta bayan yayi garkuwa da ita ya nemi kudin fansa har naira miliyan shida.

Gadai cikakken videon kusake kalla

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button