News

DÁ ƊUMÍ ƊUMÍ: Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya Angwance Da Safiyar Wannan Rana

DÁ ƊUMÍ ƊUMÍ: Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya Angwance Da Safiyar Wannan Rana

Da safiyar wannan rana ta Juma’a 6 ga watan 1 na shekara ta 2023 aka ɗaura Auren Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Amaryarsa Hauwa’u Adamu Abdullahi Dikko.

An Daura Auren ne a gidan marigayi Jarman Kano Farfesa Isah Hashim dake unguwar Nassarawa a birnin Kano.

Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani Cigari shine ya kasance wakilin Mai Martaba Sarkin Kano, yayin da Alhaji Shehu Hashim ya kasance a matsayin waliyyin Amarya.

Amaryar wadda ake kira da Hajiyayye, an riga da anyi mata baiko da Mai Martaba Sarkin na Kano ne tun cikin shekarar da ta gabata, wanda ya kasance aka Daura Auren da safiyar wannan rana, kuma ta kasance guda daga cikin zuri’ar marigayi Malam Jamo dan’uwan marigayi Sarkin Kano na 2 a daular Sarakunan Fulani Malam Ibrahim Dabo.

Mahalarta taron Daurin Auren sun hada da Makaman Bichi Alhaji Isyaku Umar tofa da Sarkin Dawaki Mai Tuta na Kano Alhaji Bello Abubakar Tuta da Dan Ruwatan Ringim da sauran mahalarta da dama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button