News

Da ɗumi-ɗumi: Wani Ƙani ya dirƙawa matar yayansa Amarya sabuwa fil ciki a Nasarawa.

Da ɗumi-ɗumi: Wani Ƙani ya dirƙawa matar yayansa Amarya sabuwa fil ciki a Nasarawa.

Daga Barrista Nuraddeen Isma’eel.

Ƙani mai suna David, ya dirƙawa matar yayansa ciki a ƙaramar hukumar Doma Jihar Nasarawa. bayan yayan nasa ya tafi samun horo na wata tara domin zama Ɗan sanda.”

“Rahoton ya cigaba da cewa, yayan na sa mai suna “Japhet” ya yi sabuwar amarya inda suka yi alƙawarin ba za su kusanci juna ba har sai ya dawo samun horo na zama cikakken Ɗan sanda.”

Bayan tafiyar “Japhet” ɗin zuwa samun horo ba wuya na zama Ɗan sanda, sai ƙaninsa “David” ya Yi amfani da wannan damar na wurin maye gurbin yayansa ɗin suna goge raini tsakaninsa da matar yayansa ɗin inda har sai da ta ɗauki ciki.”

Bugu da ƙari bayan dawowar “Japhet” jihar Nasarawa zuwa gida a domin duba iyali kawai sai yayi kaciɓis da wannan mummunar lamari, matarsa ɗauke da ciki rugum har na wata tara, biyo bayan tsananta bincike da aka yi bayanai suka tabbatar cewa ƙaninansa ne “David” ya dirƙawa mata ciki.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button