News

DA DUMI-DUMI: Ankama Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu Da Matarsa, Beatrice Nwanneka Bisa Safarar Sassan Dan Adam

DA DUMI-DUMI: Ankama Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu Da Matarsa, Beatrice Nwanneka Kan Safarar Sassan Mutum

Ana tuhumar tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice Nwanneka a kasar Burtaniya bisa laifin hada baki wajen safarar wani yaro zuwa kasar turai domin cire wasu sassa a jikinsa.

Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya ta ce an tsare ma’auratan a gidan yari kuma za su bayyana a Kotun Majistare ta Uxbridge a ranar Alhamis, 23 ga watan Yuni.

An tuhume su da laifin hada baki don shirya ko saukaka tafiyar wani yaro da nufin yin amfani da sassan jikinsa.

Sanarwar da rundunar ‘yan sandan ta fitar ta ce, “An kaddamar da binciken ne bayan an sanar da jami’an binciken laifukan da za su iya faruwa a karkashin dokar bautar zamani a watan Mayun 2022.

“An kiyaye yaro kuma muna aiki tare da abokan hulɗa a kan ci gaba da tallafawa. “Kamar yadda ake gudanar da shari’ar laifuka a yanzu, ba za mu ba da ƙarin bayani ba.”

Sai dai ba a bayyana jinsi ko shekarun yaron ba, haka kuma ba a bayyana inda aka kama shi ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button