News

Da Dumi-Dumi Yan Bindiga Sun Sace Mutane 40 A Masallaci A Katsina Suna Sallar Tahajjud

Rahotanni Daga Jihar Katsina Na Cewa, wasu yan bindiga sun afkawa wani masallaci tare da sace sama da mutum 40.

Haka zalika rahoton ya kara da cewa an sace mutanen ne da tsakar dare A Masallaci a lokacin da suke yin sallar tahajjud.

Shaidun su kara da cewa yan bindigar sun sace mutanen ne batare da sunyi harbi ba, har suka kammala.

Dafarko dai masu garkuwan sun tafi da mutane arba’in da bakwai. Sai daga bisani bakwai din suka dawo. Kamar yadda aka shaidawa jaridae dailynigerian.

Kazalika Wani mazaunin garin mai suna Lawal Jibiya, ya ya bayyana cewa. Sun samu sanarwa daga mazauna kauyukan game da harin, bayan sun ga motsin ‘yan bindigar da ke kan hanyar zuwa garin.

Ya cugaba da cewa daruruwan matasa da kungiyar ‘yan banga da ke cikin garin suna cikin shirin ko ta kwana don tunkarar ‘yan ta’addan,

amma maharan suka sauya hanyarsu suka shiga garin daga mashigar yamma.

Anan Muke Addu’ar Allah Ya Bayyanasu Ya Dawo Dasu Gida Lafiya Amin.

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button