News

DA DUMI’DUMI: Yanzu-yanzu ‘Yan bindiga sun Kai hari gidan yarin Kuje dake babban birnin tarayya Abuja.

DA DUMI’DUMI: Yanzu-yanzu ‘Yan bindiga sun Kai hari gidan yarin Kuje dake babban birnin tarayya Abuja.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan ta’adda ne a halin yanzu suna kan kai hari a gidan gyaran hali na Kuje da ke Abuja, babban birnin tarayya.

Majiyoyi da dama sun shaida wa majiyarmu cewa ‘yan bindigar sun kai farmakin ne da misalin karfe 10 na dare amma jami’an tsaro sun samu nasarar dakile harin.

Kuna iya jin karar harbe-harbe, muna fuskantar mummunan hari,” in ji daya daga cikin majiyoyin.

An kafa gidan yarin Kuje a cikin 1989, yana da mafi ƙanƙanta kuma mafi girman ɗakunan da ake tsare da fursunoni.

Ya shahara wajen rike manyan mutane da suka hada da tsofaffin gwamnoni da ministoci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button